24 Disamba 2015 - 09:01
"Maciya amanar kasa: Ko kudi ko dauri"

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ya dauki aniyar magance matsalar cin hanci da rashawa haikan, domin in ba haka ba kasar za ta durkushe.

A saboda haka ya ce, za a tilastawa mutanen da a ka samu sun kwashe kudin gwamnati, ko dai da sunan sayo makamai, ko kuma yin wasu ayyuka, in ba haka kuma za a daure su.288